✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kona ofishin yakin neman zaben Atiku a Gombe

Mun yi mamaki don mun san dai babu tsamin dangartaka tsakanin Atiku da Gwamna Inuwa Yahaya.

Wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun bi dare inda suka cinna wuta a ofishin yakin neman zaben tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar na shiyyar Arewa maso Gabas da ke Jihar Gombe.

Haka kuma maharan sun kone babbar sakatariyar jam’iyyar PDP a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai a Gombe, Shugaban kungiyar ’yan kasuwa da suke yakin neman zaben Atiku a 2023 Dokta Ali Bappayo Adamu, ya ce maharan sun yi musu barna a ofis din kana suka sace na’urar sanyaya daki wato AC da sauran abubuwa masu amfani da suka yi awon gaba da su.

Ya ce “cikin dare masu gadi su suka bugo mana waya kan cewa ga wasu gungun matasa sun kawo hari amma la’akari da yawansu su kansu suka tsere.”

Dakta Ali Bappayo, ya ce babu wanda suke zargi amma dai suna kira mahukunta masu ruwa da tsaki da su zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika.

A cewarsa, “muna son wadanda suka aikata wannan abu su fuskanci hukunci domin mun san cewa tsakanin mai gidanmu Atiku Abubakar da Gwamna Inuwa Yahaya babu wata matsala.

“Mun yi mamaki gaskiya don a iya saninmu babu wata tsamin dangartaka tsakanin gwamna da mai gida amma sai gashi wasu matasa da ba a san ko su waye ba sun zo sun yi mana barna.”

A cewarsa, wannan ofishi na ’yan kasuwa ne masu neman Atiku ya fito takara da ake kira North East Business Communities Atiku for president 2023 (NEBCO) wanda aka bude shi kimanin watanin uku da suka gabata da ya kunshi ’ya’yan kowacce jam’iyya ba PDP kadai ba.

A bangaren jam’iyyar PDP kuwa shugaban Jam’iyyar Janar Audu Kwaskebe mai ritaya, ya shaida wa ’yan jaridar cewa wasu mahara ne suka kai wa sakatariyar ta su hari inda suka farfasa komai sannan suka banka mata wuta.

Kwaskebe, ya ce yanzu haka suna bincike don gano cikakken bayanin da zai ba su damar dakile faruwar hakan nan gaba.

Sai dai ya roki ’ya’yan jam’iyyar da cewa kar su ce za su dauki mataki akan wata jam’iyya saboda basu tabbatar da wadanda suka aikata hakan ba.

Kazalika, ya ce Kwamsihinan ’yan sandan jihar, Ishala Babatunde Babaita, ya ziyarci sakatariyar ta su da kansa don ganewa ido sa abin da ya faru kuma ya yi musu alkawarin cewa za su dauki matakin da ya dace.

Sai dai hakar wakilinmu ba ta cimma ruwa ba, wanda ya nemi jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Mary Malum.