✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kone gidaje 10, sun kwashi abinci a kauyen Kano

Maharan sun kai farmaki a Dan Jamfari ta kauyen Barbaji da ke Karamar Hukumar Rogo a Jihar Kano.

Maharan sun kai farmaki a Dan Jamfari ta kauyen Barbaji da ke Karamar Hukumar Rogo a Jihar Kano.

Wani mazaunin kauyen mai suna Magaji Audu ya ce, maharan da yawansu ya kai kimanin 200 dauke da muggan makamai sun shigo kauyen ne da tsakar dare.

“Sun shigo ne dauke da sanduna da adda suna bi gida-gida wai su na neman wani babur da aka sace.

“Sun yi kokarin su sare ni a gaban iyalina idan ban fito musu da ’ya’yana ba, wadanda suka ce sun sace musu babur,” in ji Malam Audu.

Ya ce, bayan nan ne sai suka dawo washegari da dare a inda suka sa wa gidansa wuta, iyalansa suka gudu.

Maharan kuma suka shiga kwashe kayan abinci da kaji da talotalo da sauran kayan noma bayan su kone gidaje 10 a kauyen.

Hakimin Rogo Alhaji Muhammadu Maharazu ya tabbatar wa da Vanguard  afkuwar lamarin.

Hukumar agajin gaggawa ta Jihar Kano ta kai wa mutanen kauyen kayan agaji a ranar Juma’a.

Shugaban karamar hukumar Dakta Saleh Jilli, ya ce, gwamanti za ta zagulo wadanda suka aikata wannan zalunci ta kuma hukunta su.