✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun sace Ba’Amurkiya a Burkina Faso

Ba’amurkiyar ta shafe shekara shida tana aiki a kasar

Hukumomin Majami’ar yankin Kaya da ke Arewacin kasar Burkina Faso sun tabbatar da sace wata Ba’amurkiya mai shekara 83 a duniya, da ke aiki da su.

Maharan sun kai hari Majami’ar ne a ranar Litinin, yayin da ake tsaka da gudanar da harkokin ibada.

Babban limamin Majami’ar, Theophile Nare, ne ya bayyana sacewar, inda ya ce an yi ta ne a cikin dare, lokacin da ’yan bindigar suka ziyarci Majami’ar, kana suka sace matar mai suna Suellen Tennyson.

Tennyson ta kwashe shekara shida tana aiki a garin Yalgo da ke kasar tun daga 2014.

Ya zuwa yanzu, babu wata kungiyar da ta dauki alhakin sace Tennyson a yankin na Arewacin Burkina Faso mai fama da tashin hankalin da yayi sanadiyar hallaka mutane sama da 2,000 da kuma tilasta wa kusan miliyan biyu barin muhallansu tare da tserewa.

Matsalar tsaro dai na ci gaba da kamari a wasu yankunan kasar, lamarin da a baya-bayan nan ya sa gwamnatin rikon kwaryar dakarun soji, ta shirya kulla kawancen soji da wasu kasashen don kawo karshen ayyukan ’yan ta’adda a kasar.