Mahara sun sace diyar Dan Majalisar Kano | Aminiya

Mahara sun sace diyar Dan Majalisar Kano

    Sani Ibrahim Paki

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace diyar dan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar Danbatta, Murtala Musa Kore.

Dan majalisar ya tabbatar da cewa masu garkuwar sun zo ne da niyyar daukar shi, amma da ba su same shi ba sai suka dauke ‘yar tasa, ko da dai ya ce har yanzu ba su tuntube su ba.

“Sun fada wa mata na cewa sun zo ne su yi garkuwa da ni, kuma duk runtsi ba za su tafi hannu-rabbana ba, shi ne suka dauke ‘yata suka tafi da ita”, inji dan majalisar.

Masu garkuwar sun dauke yarinyar ‘yar aji na biyu a babbar sakandare ne da sanyin safiyar Lahadi, “Lokacin ina Kano aka kira ni daga gida da misalin karfe 2:30 na dare aka shaida min an dauke Juwairiyya.

“Lokacin da masu garkuwar suka mamaye gida na sun daure yayana, Lawal Kore wanda suka yi zaton ni ne da farko.

“To sai dai da ya shaida musu ba na gida sai suka shiga bangaren da iyalai na suke don su tabbatar.

To sai dai zuwa lokacin hada wannan rahoton rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ba ta tabbatar da lamarin ba.