✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun sace matar aure da danta

'Yan bindiga sun yi awon gaba da matar da danta bayan mijinta ya tsere

‘Yan bindiga da ke zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wata matar aure da danta bayan tserewar mijinta a lokacin da maharan suka kai masa farmaki a gidansa da ke yankin Chaza a Garin Suleja ta jihar Neja.

‘Yan bindigar su kuma sace wani jami’in gwamnati mazaunin garin da wani shugaban jam’iyya gabanin kai hari a gidan mijin matar.

Kwamnadan ’yan sanda na yankin Suleja ACP Sani Badarawa
ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce suna yin dukkan mai yiwuwa
don kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su din cikin koshin lafiya.

Mijin matar ya samu tserwa na bayan ya diro daga kan benen gidansa mai hawa daya kafin maharan su cimmasa.

Aminiya ta samu labarin cewa bayan harbe-harben da aka yi ta yi da misalin karfe 1 na daren Lahadi, wata mota da ake kyautata zaton masu garkuwa da matar ne ta fice daga yankin a cikin tsananin gudu.