✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun sace shanu da rana tsaka a Jibiya

Maharan sun shiga kauyen da rana tsaka sannan suka kada shanun mutane.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu shanu da rana tsaka a kan hanyar Katsina zuwa Jibiya.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa, an ga ‘yan bindigar dauke da bindigogi suna tafiya a kan titin tare da dabbobin a wani wurin da suka kai wa wata motar bas mallakin Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina (KTSTA) hari.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya ce jami’an tsaro na binciken lamarin.

A yayin harin bas din da aka kai a ranar Lahadin da ta gabata, rahotanni sun ce ‘yan ta’addar sun kashe direban tare da raunata wasu yayin da suka yi awon gaba da wasu fasinjojin kayayyakinsu.

Hare-haren ‘yan bindiga ba sabon lamari ba ne musamman a yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya.