✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun sace shugaban karamar hukuma, sun harbe dogarinsa

Masu garkuwa da shugaban karamar hukumar na neman kudin fana Naira miliyan 30.

’Yan bindiga sun sace Shugaban Karamar Hukumar Keffi ta Jihar Nasarawa, Baba Shehu, tare da harbe dogarinsa, Alhassan Habeeb, har lahira.

Hakan ya faru ne ranar Juma’a da dare a hanyar Akwanga zuwa Gudi a ranar juma’ar a lokacin da suke kan hanyarsu ta komowa Keffi daga Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa.

Mataimakin Daraktan Walwalar Jama’a na Karamar Hukumar Keffi, Alhasaan Nasir ya tabbatar da rasuwar dogarin shugaban karamar hukumar.

Rahotanni daga jihar sun ce maharan sun kira suna neman a biya su Naira miliyan 30 kafin su sako Shugaban Karamar Hukumar Keffin tare da direbansa, Tanimu Senior Man da suke hannunsu.

Ya bayyana cewa an yi garkuwa da shugaban karamar hukumar ne tare da hadiminsa na musamman.

A ’yan kwanakin nan dai rahotanni sun nuna masu garkuwa da mutane sun matsa wa  hanyar Gudi zuwa Akwanga inda suka yawaita kai hare-hare a yankin.