Mahara sun yi awon gaba da Kwamishina a Bayelsa | Aminiya

Mahara sun yi awon gaba da Kwamishina a Bayelsa

Yan-Bindiga
Yan-Bindiga
    Bassey Willie, Yenagoa da Abubakar Muhammad Usman

Wasu mahara a Jihar Bayelsa sun yi awon gaba da Kwamishinan Kasuwancin Jihar, Mista Otokito Oparniola.

Rahotanni sun ce maharan sun yi garkuwa da Kwamishinan ne a daren Alhamis, a gidansa da ke Otuokpoti a Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar.

Aminiya ta rawaito yadda maharan suka shiga yankin da misalin karfe 11:00 na dare, inda suka tsorata mutane da harbi sannan suka shiga gidansa kai tsaye tare da yin garkuwa da shi.

Ko da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’Yan Sandan Jihar, SP Asinim Butswat, ya ce yana dakin taro amma zai tuntubi wakilinmu daga baya.

Idan ba a manta ba, ko a watan Disamban 2021 sai da wasu ’yan bindiga suka kashe wasu ma’aikatan kamfanin mai na Agip a Karamar Hukumar Nembe ta Jihar.