✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun yi awon gaba da matar Dagaci a Kebbi

’Yan bindiga sun tafi da matar basaraken bayan sun neme shi sun rasa.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da matar Mai unguwar kauyen Nayelwa a a Karamar Hukumar Kalgo ta Jihar Kebbi.

Maharan sun far wa kauyen Nayelwa ne tun da sanyin safiyar Juma’a kowannensu dauke da muggan makamai.

Majiyoyi sun ce da zuwar ’yan bindigar suka wuce kai tsaye zuwa gidan basaraken, Muhammadu Kabir, suna neman shi.

Shaidu sun tabbatar cewa maharan sun shafe sama da awa daya a garin suna neman basaraken, amma ba su gan shi ba, daga nan suka tafi da daya daga cikin matansa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, ya shaida wa wakilinmu cewa zai tuntube shi daga baya domin karin bayani.