✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maharan sun harbe shugabannin PDP biyu a Filato

Maharan sun harbe shugabannin PDP biyu ne a yayin da suke tare da dan majalisa mai wakiltar Jos ta Aewa da Bassa.

Mahara sun harbe wasu shugabannin jam’iyyar PDP biyu a Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato har lahira.

An kashe shugabannin ne a lokacin da dan majalisar mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa/Bassa a Majalisar Dokokin Jihar Filato, Hon Musa Agha, ya kai ziyarar aiki a karamar hukumar.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun lalata motar dan majalisar.

Ya ce ana ci gaba da bincike don gano wadanda suka kai harin.

Kabilar Iregwe da ke Bassa ta yi Allah wadai da harin tare da yin kira ga jami’an tsaro da su gano wadanda suka kai harin.

Kazalika, jam’iyyar PDP a jihar ta yi Allah tir da harin, inda ta ce al’ummar jihar na cikin hatsari duba da yadda ake kai hari kan jama’a ba gaira ba dalili.