✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaukaciyar guguwar ‘Ian’ ta raba Amurkawa 2.5m da muhallansu

Guguwar dai na gudun kilomita 241 a kowane awa

Mahaukaciyar guguwar nan ta ‘Ian’ da kuma mummunar ambaliyar ruwa sun ritsa da akalla mutum miliyan biyu da rabi a gidajensu a jihar Florida da ke Amurka.

Tuni dai hukumomi suka ce sun fara kiyasta girman barnar da guguwar ta yi, wacce tana daga cikin irinta mafiya muni a Amurka a ’yan shekarun nan.

Rahotanni sun ce a ranar Alhamis guguwar ta yi sanadiyyar lalacewar wutar lantarki sannan sabis din kamfanonin waya ya dauke, lamarin da ya sa mutane ba sa iya kiran waya don su nemi taimako.

Ya zuwa yanzu dai, hukumomi sun tabbatar da mutuwar wani tsoho mai shekara 72, wanda ya mutu a garin Deltona, yana kokarin tsira daga mamakon ruwan saman, kamar yadda ofishin Shugaban karamar hukumar Volusia ya tabbatar.

Kazalika, wani kwalekwale da ke dauke da wasu ’yan ci-rani na kasar Kyuba ya nitse a ranar Laraba. Daga bisani jami’an ceto sun sami nasarar ceto mutum uku, amma har yanzu ana neman wasu guda 20.

Gwamnan jihar ta Florida, Ron DeSantis, ya ce yanzu haka akwai wasu mutane da ba a san adadinsu ba da suka makale a yankunan da ambaliyar ta mamaye bayan sun ki bin umarnin masu aikin ceto.

A yankin Collier kuwa, yanzu haka an fara amfani da dogayen karafa masu tafiya wajen ceton mutane.

Guguwar dai tuni ta wuce matakin aji na hudu kuma tana gudun kilomita 241 a kowanne awa tun lokacin da ta fara, kuma ita ce ta biyar mafi muni a tarihin Amurka.

Shugaban Kasar, Joe Biden, ya ayyana ta a matsayin wata annoba, kuma ya ba da umarnin yin amfani da dukkan kayan da ake da bukata na Gwamnatin Tarayya a yankunan da ta shafa.