✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai ciki da karamin yaro sun mutu a hatsarin mota

Rahotanni sun bayyana cewa wata mata mai juna biyu mai suna Endurance da danta mai shekara biyu sun mutu a wani hatsarin mota da ya…

Rahotanni sun bayyana cewa wata mata mai juna biyu mai suna Endurance da danta mai shekara biyu sun mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a titin Isiokolo da ke Jihar Delta.

Hatsarin ya rutsa da matar mai shekara 19 da dan nata ne a ranar Lahadi lokacin da wata mota da ake zargin kwaceta aka yi ta afka musu.

Wani ganau ya ce “tsautsayin ya faru da su ne bayan sun tafi kasuwa sayen kayan abinci.

“Motar ta kwace ne ta hau kansu kuma nan take suka mutu kuma ba karon farko ba ke nan da suka fara zuwa kasuwa siyayya”, inji shi.

Wani jami’in dan sanda dake ofishin ’yan sanda na Isiokolo, wanda ba a bayyana sunansa ba ya tabbatar da aukuwar hatsarin.