✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai gidan talabijin na AIT da iyalansa 7 sun kamu da coronavirus

Mamallakin kamfanin yada labarai na Daar Communications wanda ke da gidan talabijin na AIT da wasu tashoshin radiyo na FM, Cif Raymond Dokpesi, ya kamu…

Mamallakin kamfanin yada labarai na Daar Communications wanda ke da gidan talabijin na AIT da wasu tashoshin radiyo na FM, Cif Raymond Dokpesi, ya kamu da cutar coronavirus, haka ma matar dansa da iyalansa shida.

Sakamakon gwajin da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta yi wa Dokpesi da iyalan gidansa bakwai ya nuna cewa dukkaninsu suna dauke da cutar.

Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan da dansa, wanda shi ne shugaban kamfanin, Raymond Dokpesi Junior, ya kamu.

Tuni dai jami’an Hukumar ta NCDC suka kwashe su zuwa cibiyar killace wadanda suka kamu da cutar ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja, inda a nan ne aka killace dan nasa tun da fari, ake  kula da lafiyar shi.

A lokacin da jami’an hukumar ta NCDC suka isa gidansa domin tafiya da shi, Cif Dokpesi ya ce yana cikin koshin lafiya, kuma ba ya tattare da damuwa.

Jami’an hukumar sun yi feshin magani a daukacin ginin kamfanin na Daar Communications da ke yankin Asokoro a Abuja.

Kamfanin na Daar ne ya mallaki gidan talabijin na AIT da tashoshin FM ta Raypower wadanda ke cikin tashoshin talabijin da rediyo masu zaman kansu mafi dadewa a Najeriya.