✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai hikima da mugu (1)

Karin maganar Sulaimanu ke nan. Da mai hikima abin fariya ne ga mahaifinsa, amma wawa yakan jawo wa mahaifiyarsa bakin ciki. Abin da ka samu…

Karin maganar Sulaimanu ke nan. Da mai hikima abin fariya ne ga mahaifinsa, amma wawa yakan jawo wa mahaifiyarsa bakin ciki. Abin da ka samu ta hanyar zamba ba zai yi albarka ba, amma gaskiya za ta cece ka. Ubangiji ba zai bar mutumin kirki da yunwa ba, amma zai hana mugu ya kai ga biyan bukatarsa. Ragwanci zai sa talauci, amma yin aiki sosai zai arzuta ka. Mutum mai hankali yakan tattara amfanin gona da kaka, amma abin kunya ne a yi barci a lokacin girbi. Mutumin kirki yakan karbi albarka, maganganun mugun kuwa sukan boye mugun halinsa. Tunawa da mutumin kirki albarka ce, amma nan da nan za a manta da mugaye. Mutane masu hankali sukan bi shawarar kirki, masu maganar wauta kuwa za su lalace. Amintaccen mutum zai zauna lafiya ba abin da zai same shi, amma marasa aminci za a kama su. Mutumin da ya ki fadar gaskiya yana haddasa wahala, amma wanda ya bayyana gaskiya zai kawo salama. Kalmomin mutumin kirki mabubbugar rai ne, amma kalmar mugun takan boye makircinsa. Kiyayya takan haddasa wahala, amma kauna takan kyale dukan laifuffuka. Mutane masu fasaha sukan yi magana mai ma’ana, amma wawaye suna bukatar horo. Mutane masu hikima sukan nemi ilimi iyakar iyawarsu, amma sa’ar da wawa ya yi magana, wahala tana kusa. Wadata takan kiyaye attajiri, amma tsiya takan hallaka matalauci. Sakayyar da za a yi wa mutumin kirki ta rai ce, amma zunubi yakan sa a kara yin wani zunubi. Mutumin da ke kasa kunne sa’ar da ake kwabarsa zai rayu, amma duk wanda bai yarda da kuskurensa ba yana cikin hadari. Mutumin da ke fadar karairayi makiyi ne, dukkan wanda ke baza jita-jita wawa ne. Bisa ga yawan surutunka, mai yiwuwa ne kwarai ka yi zunubi, amma idan kai mai la’akari ne, sai ka yi shiru. Kalmomin mutumin kirki suna kama da azurfa tsantsa, amma shawarwarin mugu ba su da wani amfani. Kalmomin mutumin kirki za su amfani mutane da yawa, amma kana iya hallaka kanka da wauta.

Albarkar Ubangiji takan arzuta mutum, amma yawan aiki ba shi yake kawo arziki ba. Wawa ne ke jin dadin aikata mugunta, amma mai fasaha yana jin dadin hikima. Abin da mugun yake tsoro, shi yakan auko masa, amma adali yakan samu biyan bukatarsa. Hadari yakan taso ya wargaza mugaye, amma amintattu lafiya lau suke a koyaushe. Sam, kada ka sa malalaci ya yi maka wani abu, zai sa ka ka yi fushi, idanunka su cika da hawaye mai zafi. Ka ji tsoron Ubangiji za ka rayu, ka yi tsawon rai, amma mugaye sukan mutu tun kwanansu bai kare ba. Abin da mutanen kirki ke sa zuciya yakan kai su ga murna, amma mugaye ba su da wani abu da za su sa zuciya a kai. Ubangiji Yana kiyaye marasa laifi, amma Yakan hallaka masu mugunta. Kullum adalai sukan yi zamansu lafiya, amma mugaye ba za su zauna a kasar ba. Maganar adalai ta hikima ce, amma harshen da ke furta mugunta, za a dakatar da shi. Adalai sun san irin maganar da ta cancanta su fada, amma mugaye, kullum sukan fadi maganar da za ta cutar.

Ubangiji Yana kin masu yin awo da ma’aunin zamba, amma Yana farin ciki da masu yin awo da ma’auni na gaskiya. Masu girman kai za a kunyatar da su nan da nan. Hikima ce mutum ya zama mai kamewa. Mutanen kirki su ne gaskiya takan bi da su. Rashin aminci kuwa yana hallaka maciya amana. Dukiya ba ta da wani amfani a ranar mutuwa, amma adalci zai hana ka mutuwa. Gaskiya takan sa zaman mutanen kirki ya zama a sawwake, amma mugun mutum shi yake kada kansa da kansa. Adalci yakan ceci amintaccen mutum, amma marar aminci, hadamarsa ce take zamar masa tarko. Mugun mutum yakan mutu da burinsa. Dogara ga dukiya bai amfana komai ba. Akan kiyaye adali daga wahala, amma takan auko wa mugu. Mutane sukan sha hasara ta wurin maganar marasa tsoron Allah, amma hikimar adalai takan yi ceto. Birni yakan yi farin ciki saboda wadatar mutanen kirki, akwai kuma sowa ta farin ciki sa’ar da mugaye suka mutu. Biranen da adalai ke cikinsu sukan kasaita, amma maganganun mugaye sukan hallakar da su. Wauta ce a yi wa wadansu maganar raini, amma mutum mai la’akari yakan kame bakinsa. Ba wanda zai yarda ya fadi asirinsa ga matsegunci, amma za ka amince wa amintaccen mutum. Al’ummar da ba ta da masu ja mata gora, za ta fadi. Yawan mashawarta yake kawo zaman lafiya. Wanda ya daukar wa bako lamuni zai yi da-na-sani, zai fi maka sauki idan ba ruwanka. Mace mai mutunci abar girmamawa ce, amma azzalumai za su samu dukiya. In ka yi alheri, kanka ka samar wa tagomashi, in kuwa ka yi mugunta, kanka ka cutar. A ainihi mugaye ba su cin ribar komai, amma idan ka yi abin da ke daidai, ka tabbata za a saka maka da alheri. Mutumin da ya yi niyyar aikata abin da ke daidai zai rayu, amma mutumin da ya dukufa ga aikata mugunta zai mutu. Ubangiji Yana kin masu muguwar niyya, amma Yana murna da wadanda ke aikata abin da ke daidai! Ka tabbata fa za a hukunta mugaye, amma ba za a hukunta adalai ba. Komai kyan mace idan ba ta da kan gado, tana kamar zoben zinare ne a hancin alade. Abin da mutanen kirki suke so kullum yakan jawo alheri, idan mugaye sun samu biyan bukatarsu kowa zai yi bacin rai. Wadansu mutane sukan kashe kudinsu hannu sake, duk da haka arzikinsu sai karuwa yake yi. Wadansu kuwa saboda yawan tsumul-mularsu sukan talauce. Ka yi alheri za ka arzuta. Ka taimaki wadansu, su kuma za su taimake ka.

(Karin Magana 10, 11-25).