✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mai horaswa ya rasu ana tsaka da wasa a Masar

Kocin ya rasu ana tsaka da wasa sakamakon bugun zuciya da ya samu.

Kocin kungiyar kwallon kafa ta El-Magd da ke kasar Masar, Adham El-Selhadar ya rasu yayin da kungiyarsa ta zura kwallo a ranar Alhamis.

An dai dauke kocin zuwa asibiti bayan da kungiyarsa ta zura kwallo a minti na 92 a ragar El Zarqa.

Bayan tabbatar da rasuwarsa a asibiti sakamakon bugun zuciya da ya samu, tuni manyan kungiyoyi na kasar irinsu Al Ahly suka shiga mika sakon ta’aziyyarsu.

Adham El-Selhadar, ya lashe gasar Firimiya ta kasar Masar lokacin da ya ke taka leda da kungiyar Ismaily SC.

Bayan rasuwarsa, kungiyar El Magd ta bayar da hutun kwanaki shida don alhinin rasuwar kocin.