✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mai jego da jariri sun kubuta daga hannun ’yan bindiga

Yadda aka fanshi jariri da mai jego daga hannun ’yan bindiga a Jibia

Mace biyu da wani jariri sun kubuta daga hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina.

A kwanakin baya ne rahotanni suka nuna mahara sun yi awon gaba da wasu mata biyu cikinsu har da mai danyen jego, ba tare da sun bari ta dauki ko abun rufe jaririn ba.

Wakilinmu ya ce an garzaya da matan da aka sako zuwa asibiti, yayin da mawuyacin halin da mai jegon ke cikin ke karuwa.