✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai jego ta sayar da jaririyarta N10,000

Ta ce ta yi haka ne saboda ta wahala matuka a yayin rainon cikin.

Wata mata mai danyen jego ta sayar da jaririyar da ta haifa a kan N10,000 washegarin ranar da ta haihu.

Matar ta shaida wa jami’an tsaro cewa ta sha wahala matuka yayin rainon cikin, shi yasa ta yanke shawarar sayar da jaririyar.

Bayan jami’an tsaron Amotekun na Jihar Ondo sun cafke mai jegon ne  ta bayyana cewa wani limamin coci ne ya sayi jaririyar kwana daya bayan haihuwarta.

Matar mai shekara 22 ce ta sayar da jaririyar ne don ba za ta iya kula da ita ba, saboda  tunda mahaifin jaririyar ya samu labarin cewa tana dauke da juna biyu ya tsere ya bar ta.

Ta ce da farko ya yi mata alkawarin zai bude mata shago, kuma a dalilin hakan ne ya yi mata ciki, amma ya tsere ya bar ta bayan ta sanar da shi tana dauke da cikinsa.

Limamin cocin da ya sayi jaririyar ne ya sanar da jami’an Amotekun game da lamarin, inda ba su yi wata-wata ba wajen cafke matar.

Wata majiya ta bayyana cewa limamcin cocin ya ba ta N10,000, wanda a cewarta a ciki za ta biya likitan da ya kula da ita yayin rainon cikin N5,000.

Malamin cocin ya ce ya ba ta kudin ne saboda gudun kada ta sayar da jaririyar ga wani mugun iri.

Daga bisani an mayar da wadda ake zargin Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke garin Ondo, don ci gaba da bincike a kan lamarin.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Ondo, Tee-Leo Ikoro, ya ce ba shi labarin faruwar lamarin, amma da zarar labarin ya iske shi zai yi wa wakilinmu karin bayani.