✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai kokarin sayar da ’yar cikinsa kan N20m ya shiga hannu a Binuwai

Wata babbar kotun yanki a Makurdin jihar Binuwai ta bayar da umarnin tsare wani mutum da aka gurfanar a gabanta a bisa kokarin sayar da…

Wata babbar kotun yanki a Makurdin jihar Binuwai ta bayar da umarnin tsare wani mutum da aka gurfanar a gabanta a bisa kokarin sayar da ’yar cikinsa kan Naira miliyan 20.

’Yan sanda ne suka gurfanar da mutumin da abokinsa, bisa zarginsu da laifukan hadin baki domin aikata laifi da satar mutum da kuma safarar mutane.

’Yan sanda mai gabatar da kara, Veronica Shaage, ta sanar da kotun cewa an kama wadanda ake zargin ne a kokarinsu na sayar da wata yarinya mai shekara hudu kan Naira miliyan 20.

A lokacin da suke tsaka da kulla cinikin ne da wani mai suna Terna, ’yan sanda suka far musu, a inda wadanda ake zargin suka shiga hannu, shi kuma Terna ya cika wandonsa da iska.

Veronica ta karato sassa daban-daban na dokokin fenal kod na jihar, da masu laifin suka karya, ta kuma roki kotun da ta zartar musu da hukuncin da ya dace.

Alkalin Kotun, Dooshima Ikpambese, ta yi watsi da ikikarin masu karar na hurumin kotun na sauraron shari’ar.

Sannan ta aika da su gidan gyaran hali domin a ci gaba da tsare su har zuwa ranar daya ga watan Disamba a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraron kara.

(NAN)