✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai Martaba: Za a fara daukar sabon fim a kan tarihin Hausawa

Fim zai mayar da hankali a kan kyawawan al'adun Hausawa.

Shirye-shirye sun kammala tsaf domin fara daukar sabon fim a kan tarihin Hausawa mai suna Mai Martaba.

Sabon fim din, wanda wani fitaccen dan jarida kuma mai shirya fina-finai, Prince Daniel Aboki yake shiryawa zai yi amfani da jarumai kusan 300, yawancinsu sabbi, da kuma dawakai akalla 100.

Daniel ya kuma ce za su shirya fim din ne don su nuna labarai masu kyau na al’ummar Arewacin Najeriya na tarihi da ba a cika mayar da hankali a kansu ba, yana mai cewa mutanen yankin ne suka fi cancanta su bayar da labarinsu, ba wani daga waje ba.

A yayin da yake yi wa manema labarai karin haske a kan fim din a Kano ranar Asabar, Daniel ya ce, “A tsari na fina-finai a duniya, Arewacin Najeriya na da labarai musamman irin na da kamar irinsu Magana jari ce da Ruwan Bagaja da kuma tsarin masarautu da kayan kyale-kyale.

“Amma in kuka duba tsari irin na fina-finai a Najeriya da ma Afirka, da kyar namu na Arewacin Najeriya ke tasiri, musamman in aka fara fita kasashen waje.

“Muna kyautata zaton in Allah Ya yarda bisa ga tsarin da muka dauko, wannan fim na Mai Martaba, muna harsashen za mu tallata shi kuma zai shiga kowace irin gasa ta fim a duniya.

“Dalilin fim din shi ne in ba ka fadi labarinka ba, wa zai ari bakinka ya ci maka albasa? In ba ka dauki al’adarka ka tallata ta ba, wa zai yi maka? Sannan ta yaya matasa za su samu aikin yi? Wannan shi ya karkato hankalinmu a kan shirin,” inji shi.

Ya kuma ba da tabbacin cewa fim din zai yi kokari matuka wajen kare al’adun yankin, tare da amfani da kayan aiki mafiya inganci don ya yi gogayya da kowane irin fim a duniya.

Daniel ya ce lokaci ya yi da za su nuna wa duniya cewa akwai labarai da al’adu masu kyau na tarihi, ba wai kawai matsalar tsaro ko garkuwa da mutane ba.

A cewarsa, la’akari da muhimmancin garin Daura a tarihin kasar Hausa, a can za a dauki fim din.

Ya ce suna sa ran fim din zai fara shiga kasuwa nan da 10 ga watan Yunin shekarar 2022.