✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai neman takarar Sanatan Yobe ta Arewa ya maka Machina a Kotu

Abubakar Jinjiri ya ce ba za ta sabu ba a hana shi neman takara.

Daya daga cikin wadanda suka nemi takarar kujerar Sanatan Yobe ta Arewa a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Abubakar Abubakar Jinjiri ya maka Bashir Sheriff Machina a kotu, inda yake kalubalantar nasarar da ya yi a zaben fidda gwanin takarar da aka gudanar makonnin da suka gabata.

Aminiya ta ruwaito cewa, fafutikar neman tikitin takarar kujerar Sanatan Yobe ta Arewa a APC, ta sake daukar wani sabon salo bayan bijirowar wannan al’amari a ranar Juma’a.

A halin da ake ciki, Machina wanda ya yi nasara a zaben fidda gwanin takarar kujerar bayan samun kuri’u 289, na fatan ganin nasarar da ya yi bata tashi a banza ba, duba da yadda tikitin ke nema subucewa daga hannunsa ya koma wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan.

Lawan wanda ya sha kaye a zaben fidda gwanin takarar kujerar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, ya koma yana ikirarin cewa nasarar da Machina ya yi a zaben fidda gwanin takarar kujerar da yake kai a yanzu ta Sanatan Yobe ta Arewa tasa ce.

Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne jam’iyyar APC ta mika sunan Sanata Ahmed Lawan a matsayin halastaccen dan takarar kujerar Sanata Yobe ta Arewa, lamarin da ta tilasta Machina neman hakkinsa a gaban Kuliya.

Sai dai kuma bayanan Hukumar Zabe ta Kasa mai Zaman Kanta, INEC sun nuna cewa Bashir Sheriff Machina ne ya lashe zaben fidda gwanin APC na kujerar Sanatan Yobe ta Arewa.

Biyo bayan bullar wannan rahoto, an samu cewa Abubakar Jinjiri a cikin jerin dalilan da ya gabatar a gaban mai shari’a Fadima Murtala Aminu a Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu a ranar Juma’a, ya kalubalanci sahihancin nasarar Machina.

Abubakar Jinjiri ta bakin lauyansa Barista Usman Lukman Nuhu, ya shaida wa wakilinmu cewa wanda yake karewa yana kalubalantar Machina, hedikwatar jam’iyyar APC ta Jiha da ta kasa da kuma Hukumar INEC a kan cire shi sunansa daga jerin masu neman takara.

A cewarsa, an haramta wa wanda yake karewa neman takarar kujerar Sanatan Yobe ta Arewa duk da kasancewarsa a wurin zaben fidda gwanin da aka gudanar.

“Na yi imani akwai kwafin takardar sakamakon zaben fidda gwanin takarar da aka fitar kuma kowa ya gani a fili cewa babu sunan Abubakar Abubakar Jinjiri da adadin kuri’ar da ya samu a cikin jerin manema takarar.”

Barista Usman Lukman ya bayyana cewa cire sunan masu neman takara ya saba wa sashe na 84 karamin sashe na 3 da 4 na Dokar Zabe.