✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mai sana’ar zanen da ya mai da jininsa tawadar zane-zane

Rashin samun kudin sayen tawada ya sa shi amfani da jinin

Wani mai sana’ar zanezane a kasar Philippine mai suna Elito Circa yana amfani da jininsa a matsayin tawada yayin zane.

Elito mai shekara 52 ya fara zane da jininsa ne tun da dadewa kuma wannan ne ya sa mutane da dama ke yaba masa bisa yadda ya gwammace wajen amfani da jininsa sama da tawada.

Elito ya tsinci kansa ne a gidan da ke da matsakaicin hali, wanda abin da suke samu ba ya biya masu bukatunsu na yau da kullum.

A cikin wannan hali ne Elito ya zavi sana’ar zane-zane tun yana makaranta.

Rashin samun kudin sayen tawada ya sa Elito ya rika samun wasu abubuwa da za su samar da launin abin da yake so kamar ruwan tumatir da sauran abubuwa masu launi.

Kwatsam wata rana sai ya kwarzane a jiki, inda jini ya fito daga nan ne sai ya fara gwada zane da jinin nasa, inda ya ga abin ya burge shi.

Daga nan ne rauni, nakan yi amfani da jinin wajen yin zanezanena, wanda jinin ma ya fi sauran abubuwan da nake amfani da su kamawa idan na yi zanen,” in ji shi.

Ya ce, duk bayan wata uku yakan je asibiti domin a zuki jininsa a ba shi ya je ya adana saboda gudanar da aikinsa na zane.

Ya ce “Muhimmancin da na bai wa aikina ne ya sa nake amfani da jinina” Elito dai ya yi manyan zane-zane jininsa, wadanda mutane ke rububin su saboda yadda suka yaba da kyansu.