✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Mai Shari’a Adamu Bello ya zama sabon Hakimin Kankara

Sarkin Katsina ya amince da nadin bayan tsige tsohon hakimin kan alaka da mahara.

Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya bai wa tsohon Mai shari’a Adamu Bello sarautar Sarkin Pauwan Katsina kuma Hakimin Kankara.

Sanarwar bayar da sarauta da Sakataren masarautar kuma Sarkin Yakin Katsina, Bello Mamman Ifo ya sanya wa hannu, ta ce an ba sabon Hakimin Kankara Alhaji Adamu Bello, daga cikin zuri’ar Nadabo sarautar ne a ranar Asabar.

Tsohon Mai Shari’ar wanda kuma Babban Sakatare ne a Hukumar ICPC, ya samu sarautar Hakimin Kankara ce bayan tsige tsohon hakimin, Alhaji Yusuf Lawal.

An tsige tsohon Hakimin Kankara kuma Sarkin Pauwan Katsina ne bisa zargin sa da alaka da ’yan bindiga masu satar shanu da yin garkuwa da mutane gami da kisan ba gaira babu dalili.

Masarautar Katsina ta same shi da laifi ne bayan ta kafa kwamitin bincike wanda ya same shi da hannu a kan zargin da ake mashi.

Nan gaba za a sa ranar da za a yi nadin na sabon hakimin.