Mai Shari’a Bolarinwa Babalakin ya rasu yana shekara 94 | Aminiya

Mai Shari’a Bolarinwa Babalakin ya rasu yana shekara 94

    Hameed Oyegbade, Osogbo da Sagir Kano Saleh

Tsohon alkalin Kotun Kolin Najeriya, Mai Shari’a Bolarinwa Babalakin ya riga mu gidan gaskiya.

Mai Shari’a Babalakin ya rasu ne a ranar Asabar yana da shekara 94, kuma shi ne mahaifin attajirin nan Wale Babalakin.

Za a yi jana’izarsa a gidansa da ke yankin Gbongan a jihar Osun da misalin karfe hudu bisa tsarin addinin Islama.

Da yake tabbatar da rasuwar, Shugaban Al’ummar Musulmi ta Jihar Osun, Mustafa Olawuyi, ya ce bawan Allah ne mai yawan ibada a lokacin rayuwarsa wadda ya ce abar koyi ce.

Olawuyi ya roki Allah Ya jikan Mai Shari’a Babalakin, Ya kuma wa iyalansa da al’ummar Musulmin jihar juriyar rashin.