✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai shekara 101 ya kammala karatun Diploma

Ya bayyana nadamarsa game da rashin kammala karatunsa a kan lokaci

Wani tsoho mai shekara 101 da ya bar makarantar gaba da sakandare a Jihar West Virginia da ke Amurka a 1930, an ba shi takardar shaidar Diploma fiye da shekara 80 da barinsa makarantar.

Makarantar Jefferson County Schools ta West Virginia ta ce, tsohon mai suna Merrill Pittman Cooper, mai shakara 101, ya halarci Kwalejin Storer, tsohuwar
makarantar sakandare a Harper Ferry, amma ya bar makarantar a lokacin
da yake matakin karshe a makarantar a 1938 lokacin da shi da mahaifiyarsa suka yi qaura zuwa Gundumar Philadelphia da ke Jihar Pennsylvania ta Amurka saboda matsalar kudi.

Merrill, ya bayyana nadamarsa game da rashin kammala karatunsa a lokacin ziyararsa a tsohuwar Kwalejin Storer, a 2018, yana jagorantar danginsa don isa makarantar Gundumar Jefferson.

Merrill ya samu takardar shaidar karramawa ta Diploma daga Makarantar Gundumar Jefferson, a wani bikin yaye xalibai da danginsa suka halarta.

“Makarantar Jefferson County ta himmatu wajen taimaka wa kowane
dalibi, tsoho ko matashi ya cika burinsa,” inji Sufetan Makarantun Jefferson County mai suna Bondy Shay Gibson-Learn.

“Ga Mista Merrill, hakan na nufin samun takardar shaidar kammala makarantar gaba da sakandare. Muna da muradun taimakawa wajen tabbatar da wannan mafarki ya zama gaske.”