✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai shekara 25 ta haifi ’ya’ya tara

Wata mai juna biyu mai shekara 25 ta haifi ’ya’ya tara a lokaci guda.

Wata mai juna biyu mai shekaru 25 a duniya ta haifi ’ya’ya tara a lokaci guda.

Halima Cisse, ’yar kasar Mali ta haifi yan mata biyar, samari hudu ne bayan hoton cikin da aka dauka da farko ya nuna tana dauke ne da cikin ’ya’ya bakwai.

Mai jegon ta sauka ne a kasar Moroko inda gwamnatin kasarta ta dauki nauyin kai ta domin samun  kulawa ta musamman.

Haihuwar ’ya’ya tara abu ne da ba a cikga gani ne, kuma a yawancin lokacin ba dukkanninsu suka rayuwa ba.

Amma Ma’aikatar Lafiya ta Kasar Mali ta ce jariran da aka haifa bayan an yi wa mai jegon tiyata suna cikin koshin lafiya.

Ministan Lafiyan, Fanta Siby, ya taya likitocin da suka kula da ita a kasashen biyu murna bisa “nasarar da ka samu”.