✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai shekara 26 ya zama Sakataren Masarautar Jama’a 

El-Rufai ya nada matashi mai shekara 26, Muhammad Adamu Sani, a matsayin sabon Sakataren Masarautar Jama'a

Gwamnatin Jihar Kaduna ta nada matashi mai shekara 26, Muhammad Adamu Sani, a matsayin sabon Sakataren Masarautar Jama’a da ke karamar Hukumar Jema’a ta jihar.

Muhammad Adamu Sani ya karbi ragamar ne a hannun wanda ya gabace shi, Alhaji Yakubu Isa (Dokajen Jama’a).

Takardar sanarwar nadin da ke dauke da sa hannun Sakataren Hukumar Kula da Kananan Hukumomin jihar, Ya’u Sani, a madadin Shugaban Hukumar, ta bayyana cewa hakan ya dace da Sashe na 13 (1) na Dokokin Gwamnatin Jihar Kaduna kan Masarautu na 2021.

An haifi sabon sakataren ne a garin Kafanchan inda ya yi karatun Firamare a Staff School da ke karkashin Kwalejin Ilmi ta Jihar Kaduna daga shekarar 2003 zuwa 2009.

Daga nan ya wuce Kwalejin Barewa da ke Zariya daga 2010 zuwa 2014 kafin ya koma makarantar Great Standard da ke Wusasa Zariya inda ya mallaki shaidar kammala babban sakandiri (SSCE).

A shekarar 2014 zuwa 2018, Jagaba ya kammala karatun digiri na farko a Sashen Kimiyyar Siyasa ta Jami’ar Bayero ta Kano.

Bayan kammala aikin yiwa kasa hidima a Sashen Karban Koke-koke na Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Jihar Kano, ya koma Jami’ar ta Bayero inda ya yi digirinsa na biyu a fannin Public Policy and Administration (MPPA), daga shekarar 2019 zuwa 2021.

Ya taba rike Shugaban Kungiyar Daliban Manyan Makarantu na Najeriya ’Yan Asalin Masarautar Jama’a