✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai shekara 27 ya kasa samun aiki saboda yana da fuskar yara

Wani mai shekara 27 a garin Dongguan a kasar China yana shan fama wajen neman aiki, saboda fuskarsa tana nuna ta bai kai shekara 20…

Wani mai shekara 27 a garin Dongguan a kasar China yana shan fama wajen neman aiki, saboda fuskarsa tana nuna ta bai kai shekara 20 ba.

Matashin mai suna Mao Sheng, ana yi masa kallon karamin yaro da shekarunsa suka gaza ya samu aiki.

Duk lokacin da matashin ya ce, ya kai shekara 27, mutane ba su yarda da hakan, inda suke yi masa kallon bai wuce shekara 10 ba.

Sai dai yayin da wasu suke ganin hakan a matsayin wata albarka ce, saurayin yana ganin cewa ana aibanta shi, tunda hakan ya hana shi samun aiki.

Yawancin masu daukar ma’aikata ba su yarda cewa ya kai shekarun da yake ikirarin ya kai ba, kuma sukan ce ba za su dauke shi aiki ba don kada hukumomi su zarge su da sa kananan yara aiki saboda kallon shekarun kuruciyar da ake yi masa.

Mao Sheng, ya dauki hankalin jama’a a kasar China a makonnin da suka gabata, bayan wani bidiyo da aka dauka a kan titunan Dongguan da ya bazu a kafar sadarwa ta Douyin a manhajar (TikTok).

A cikin bidiyon, matashin ya bayyana shekarunsa kuma ya yi korafin cewa, ya kasa samun aikin da zai tallafa wa mahaifinsa, wanda ke samun sauki daga ciwon barayin jiki.

Ya ce ya nemi aiki a masana’antun garinsu tare da abokansa, amma yayin da su suka samu aiki nan take, shi bai yin sa’a a dauke shi ba saboda don kamanninsa.

Labarin Sheng ya taba zukatan miliyoyin mutane a China, wadanda da yawa daga cikinsu suka zargi masu daukar aiki da kin ba matashin dama saboda fuskar yara da yake da ita.

An yi sa’a, bayan labarinsa ya shahara wasu ’yan kasuwa da dama sun tuntube shi suka ba shi ayyukan yi.

Wani faifan bidiyo da aka wallafa a kafar Douyin kwanaki kadan da suka gabata ya nuna cewa, Mao ya amince da daya daga cikin ayyukan da aka yi masa ta yi, kuma yana fatar samun kudin da zai taimaka wa mahaifinsa ya murmure.

Kuma da zarar mahaifin ya murmure shi kuma yana fata ya samu budurwa da zai aura don kafa nasa iyalin.

Duk da an dauki labarin Mao Sheng a gidajen labarai da yawa a kasar China, babu daya daga cikinsu da ya ambaci dalilin da fuskar matashin ta zamo haka.

Akwai masu zargin cewa dole akwai alakar halittar da take hade da kwakwalwa wacce take sa girman jikin mutum, wanda ke sarrafa girman jiki.

Saboda an ga irin wadannan a baya, inda manya mutane suke da jikin yara, kuma irin wannan halittar ce kusan koyaushe take haddasa haka.