✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai shekara 85 ya auri mata ta 11

Ina da koshin lafiya don haka ni babu abin da zai hana ni karin aure.

Wani dattijo mai shekara 85 dan kasar Saudiyya mai kuma sha’awar aure-aure da tara ’ya’ya, ya sake daura aure da wata matar a karo na 11 domin ya cike gurbin ta hudu.

Mutumin mai suna Ali Al Balawi dan kasar Saudiya ya sake kara auren ne a karo na 11 da wata mace ’yar kasar da ba a bayyana sunanta ba.

An daura auren ne a garin Tabbuka da ke Arewa maso Yammacin kasar.

Ali na da mata uku da kuma ’ya’ya 38, wanda suka kunshi maza 18 da mata 20 da kuma jikoki 88, ya kuma kara auren ne a karo na 11 a cikin lissafin matan da ya aura kawo yanzu.

An yi walimar auren a garin nasu wanda ya samu halartar ’yan uwa da abokai da kuma dangi.

An rawaito dattijon na cewa, yana da koshin lafiya bai kuma taba gamuwa da wata larurar rashin lafiya ba inda ya ce, “don haka ni babu abin da zai hana ni karin aure”.

Bugu da kari, Ali ya kuma ce, yana da yalwar aljihu, sannan kuma Allah Ya wadata shi da lafiyar jiki da kwakwalwar da zai dauki nauyi da kuma kula da mata hudu da kuma dawainiyarsu.