✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya sayi fom din takara

Bashir Ahmad ya cike fom din takarar bayan bayyana aniyarsa ta wakilatar mazabar Gaya, Ajingi da Albasu a Majalisar Wakilai

Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan Kafofin Sada Zumunta, Bashir Ahmad, ya sayi fom din takarar dan Majalisar Wakilai a zaben 2023.

Bashir Ahmad ya bi sahun sauran ’yan takarar APC wajen sayen fom din ne a ranar Asabar domin wakiltar mazabarsa ta Gaya, Ajingi da Albasu ta Jihar Kano a Majalisar Wakilai.

Bashir na zawarcin kujerar ce tare da dan Majalisar Wakilai mai ci a mazabar, Mahmoud Abdullahi Gaya, wanda shi ma dan jam’iyyar APC ne kuma karamar hukumarsu daya.

Ana kallon Bashir Ahmad a matsayin mafi karancin shekaru a cikin hadiman Buhari, kasancewar an nada shi lokacin shekarunsa 24, bayan ya yi aiki na wasu shekaru a kafafen yada labarai na intanet.

Tun daga lokacin, matashin ya zama sananne a kafofin watsa labarai, inda ya samu mabiya sama da miliyan daya a kafar Twitter tare da abokai da mabiya masu tarin yawa a Facebook.

Sai dai sabanin sauran masu neman takarar da suka sayi fom, Bashir Ahmad bai bayyana ko saya mishi fom din aka yi ba ko shi ya saya wa kansa ba.

Da yake sanar da sayen fom din, Bashir Ahmad, ya roki Allah Ya ba shi nasara, inda jama’a da dama ke bayyana ra’ayoyi mabambanta a kansa.

Bashir ya wallafa a shafukansa na Facebook da Twitter cewar “Da sunan Allah…

“Yanzu na kammala cike fom dina, sauran ya rage a mazabata, mutanen kananan hukumomin Gaya da Ajingi da Albasu a Jihar Kano, wadanda da yardar Allah zan wakilce su a Majalisar Wakilai.

“Allah (SWT) ya ba mu NASARA!,” kamar yadda ya wallafa.

Rahotanni sun bayyana cewa Bashir ya fara zawarcin kujerar Majalisar Wakilai tun wata biyu da suka gabata lokacin da ya fara tuntubar masu ruwa da tsaki a mazabarsa.

Amma wasu da dama a mazabar tasa da ke amfani da shafin Facebook, sun soke shi kan rashin tallafa wa yankin ko matasan da suka taso tare a rayuwa.