✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai tsohon ciki da amarya na cikin daliban da aka kwashe a Kaduna

A cikin wani bidiyon da, an ga wasu daga cikin daliban suna neman taimako.

Wata mata mai juna biyu na tsawon wata shida na daga cikin daliban da aka sace a Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Afaka, Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, a daren Jumaa.

Aminiya ta ruwaito yadda ’yan bindigar suka kutsa kai cikin makarantar bayan sun rusa wani bangare na katangarta.

A cikin wani bidiyon da masu garkuwar suka fitar, an ga wasu daga cikin daliban suna neman taimako.

Daya daga cikin daliban da ta kubuta daga harin ta gano abokiyar karatunta mai suna Maman Ahmad mai dauke da cikin wata shida a cikin bidiyon.

A ciki dai, an ji wani daga cikin ’yan na bindigar umartar Maman Ahmad da ta fuskanci kyamarar kuma ta yi magana.

Da take magana da harshen Hausa, ta ce: “Salamu Alaikum, mu ne daliban Makarantar Gandun Daji ta Tarayya da aka sace shekaranjiya. Muna rokon gwamnati da ta taimaka mana. Mun ji suna cewa za su turo sojoji su taimaka su fidda mu; To don Allah su taimake mu su rufa mana asiri saboda mutanen suna cewa duk wani soja da ya fuskanci wurin, ko mutum daya daga cikinmu ba zai koma gida ba. Su taimaka wa rayuwarmu,”inji ta.

Sauran wadanda lamarin ya rutsa da su kuma sun hada da wata mai suna Rose Okoye da aka gano cewa ana shirin bikin aurenta kafin faruwar lamarin.