✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maidakin El-Rufai ba ta kamu da Coronavirus ba

Maidakin Gwamna Nasiru El-Rufai na Jihar Kaduna ta ce ba ta kamu da cutar Coronavirus ba. Hajiya Hadiza Isma El-Rufai ta bayyana haka ne a…

Maidakin Gwamna Nasiru El-Rufai na Jihar Kaduna ta ce ba ta kamu da cutar Coronavirus ba.

Hajiya Hadiza Isma El-Rufai ta bayyana haka ne a shafinta na Twitter da maraicen Litinin.

“Sakamakon gwajin da aka yi min na COVID-19 ya fito. Ba na dauke da ita. Na gode da addu’o’inku da fatan alheri”.

Wannan sako na maidakin gwamnan Kaduna yana zuwa ne dai yayin da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ke bayyana samun karin mutum biyu da suka kamu a jihar.

Ranar Asabar ne dai Gwamna El-Rufai ya wallafa wani hoton bidiyo wanda a cikinsa yake bayyana cewa sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna yana dauke da cutar.

Gwamnan, wanda ya halarci wani taro a Abuja wanda Gwamna Bala Muhammed na Jihar Bauchi ma ya halarta, ya jagoranci tabbatar da aiki da umarnin da gwamnatinsa ta bayar na rufe harkokin kasuwanci da nufin hana cutar yaduwa.