✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta rusa zaben Shugaban Masu Rinjaye Ado Doguwa

Kotun daukaka kara da ke jihar Kaduna a yau Litinin ta rusa zaben Dan Majalisar Wakilan Tarayya mai Wakiltar mazabar Tudun Wada da Doguwa na…

Kotun daukaka kara da ke jihar Kaduna a yau Litinin ta rusa zaben Dan Majalisar Wakilan Tarayya mai Wakiltar mazabar Tudun Wada da Doguwa na Jihar Kano kuma Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar, Alhassan Ado Doguwa.

Alkalan kotun karkashin jagorancin Alkali Oludotun Adefope-Okojie, ne sanar da hukuncin kotun, ya kuma umarci Hukumar zabe mai zaman kanta INEC da sake zaben mazabar daga yanzu zuwa kwanaki 90.

Dan takarar kujerar Majalisar Tarayyar na mazabar Tudun Wada da Doguwa a Jam’iyyar PDP ), Air Commodore Salisu Shehu (mai ritaya ) ne ya shigar da karar don kalubalantar nasarar zaben Ado Doguwa, inda ya zargi cewa an tafka magudin zabensa a matsayin Dan Majalisa lokacin a zaben Febrairun 2019.