✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa na son a fara hukuncin kisa kan barayin kayan jirgin kasa

Majalisar ta ce masu satar na da niyyar kisan kai, saboda za su iya sa jirgin yin hatsari.

Majalisa Dattijai ta ce tana duba yuwuwar  yin dokar da za ta tanadi zartar da hukuncin kisa kan barayin kayan jirgin kasa a Najeriya.

Shugaban Kwamitin Sufuri na Majalisar Dattijai, Sanata Abdulfatai Buhari ne ya bayyana hakan a Legas ranar Juma’a.

Dan majalisar, wanda ya koka kan karuwar satar kayan jrigin ya ce masu satar na da niyyar aikata kisan kai, saboda hakan zai iya sa jirgin ya yi hatsari.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci Kwamitin Sufuri da na Jiragen Kasa na majalisar wajen duba sabon layin dogon Legas zuwa Ibadan.

Abdulfatai, wanda ya kuma jinjina wa kokarin Gwamnatin Tarayya kan aikin, ya ce majalisar ba ta da korafi kan ciyo bashi daga ketare don yin ayyukan raya kasa.

Aminiya ta rawaito cewa akalla akwai zarge-zargen satar kayan jirgin kasa  a kotuna daban-daban na kasar nan.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC), Injiniya Fidet Okhiria ya tabbatar da cewa ko a ’yan kwanakin nan an kama mutane da dama da ake zargi da tsara kayan kuma yanzu haka an bgurfanar da su a gaban kotu.