✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa na yunkurin hana daukar masu digiri ayyukan wucin gadi a Najeriya

Majalisar Dattijai a ranar Alhamis ta fara aiki a kan wani kudiri da zai haramtawa kamfanoni masu zaman kansu da hukumomin gwamnati daukar masu digiri…

Majalisar Dattijai a ranar Alhamis ta fara aiki a kan wani kudiri da zai haramtawa kamfanoni masu zaman kansu da hukumomin gwamnati daukar masu digiri aiki a matsayin ma’aikatan wucin gadi a Najeriya.

Kudirin, wanda Sanata mai wakiltar mazabar Ondo ta Tsakiya daga jihar Ondo, Ayo Akinyelure ya gabatar a zauren majalisar ya ce dole ne a rika daukarsu a matsayin ma’aikata na dindindin ba wai na wucin gadi ba.

A cewarsa, “Daukar matasa masu digiri a Najeriya ayyukan wucin gadi wata matsala ce da ta tasamma zama ruwan dare a Najeriya a matsayin wata hanya da kamfanoni ke amfani da ita wajen cin moriyarsu daga bisani kuma su yi watsi da su.

“Alkaluma daga Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) na nuna cewa ma’aikata da dama a bangaren kamfanonin sadarwa da harkokin mai cike suke da ma’aikatan wucin gadi.

“Haka lamarin yake a bangarorin hakar ma’adinai, karafa, bankuna da kamfanonin inshora.

“A dukkan wadannan wuraren, dauka da korar ma’aikata ba wani abu bane; ba su da tsayayyen albashi ko ka’idojin aiki. Ana kaskantar da masu digirin Najeriya a gaban takwarorinsu na kasashen ketare a cikin kasarsu ta haihuwa.

“Lamarin na da alaka da karuwar matsalar rashin aikin yi, wanda shine ke sa irin wadannan kamfanonin su rika cin karensu ba babbaka saboda masu neman aikin ga su nan bila adadin,” inji Sanata Ayo.

Idan kudirin ya zama doka dai, za a rika daukar masu digirin ayyukan dindindin ne kawai a Najeriya.