✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta amince da dokar bai wa kananan hukumomi ’yancin kai

Majalisar ta amince kan bai wa kananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu.

Majalisar Dattawa ta amince da dokar ’yancin cin gashin kan kananan hukumomi da majalisun dokokin jihohi da kuma bangaren shari’a a matakan jihohi.

Wannan na daga cikin sabbin tanade-tanaden da aka samar a kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa gyaran fuska da zummar karfafa kananan hukumomin a matsayin matakan gwamnati na uku bayan gwamnatin tarayya da ta jihohi.

Yanzu haka gwamnonin jihohi sun ki sakin marar kananan hukumomin domin gudanar da ayyukansu saboda yadda kundin tsarin mulkin da ake amfani da shi na 1999 ya ba su damar sanya ido a kansu.

Wannan ya sa gwamnonin ke yin dokoki yadda suke so na tafiyar da kananan hukumomin da kuma karbe musu kudaden da suke samu daga Asusun Gwamnatin Tarayya a karkashin dokokin da suka yi na asusu guda.

Zauren majalissun ya kuma yi fatali da da bukatar bai wa Shugabannin Majalisar Dattawa da ta wakilai albashi har iya rayuwarsu.

An dai kada kuri’a kan kudurorin yi wa tsarin mulki na 1999 gyaran fuska ne ta hanyar na’ura, inda galibin ’yan majalisar suka yi ittifaki a kan abubuwan da aka rika ce-ce-ku-ce a kansu.

Tuni kungiyoyin mata suka fara nuna bacin ransu kan kin amincewa da muhimman bukatun da suka shafe su.

Kudirori 68 ne aka kada kuri’a a kansu, inda ’yan majalisar suka ki amincewa da batun bai wa shugabannin majalisun tarayyar da manyan alkalai rigar kariya.

Sun kuma yi watsi da batun bai wa mata kashi 15 cikin 100 na shugabancin jam’iyyun siyasa.

Nan gaba za a mika wa majalisun jihohi kunshin kudirorin, inda su ma za su kada kuri’ar amincewa ko akashin haka, kuma dole ne sai majalisun jihohi akalla 24 sun amince da sauye-sauyen kafin su zama doka.