✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta kara kasafin 2023 zuwa N21.82trn

Majalisar Wakilai ta amince da kasafin shekarar 2023 bayan kara yawansa zuwa Naira tiriliyan 21.82.

Majalisar Wakilai ta amince da kasafin shekarar 2023 bayan kara yawansa zuwa Naira tiriliyan 21.82.

A zamanta na ranar Laraba ne Majalisar ta kara Naira tiriliyan 1.31 a kan Naira tiriliyan 20.51 da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar mata da farko, sannan ta amince da shi.

Jimillar kasafin ya nuna an ware tiriliyan N6.55 domin biyan basuka, tiriliyan N8.3 domin ayyukan yau da kullum.

An ware biliyan N967.48 domin hukumomi da ma’aikatun gwamnati sai kuma tiriliyan N5.97 domin manyan ayyuka, daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Disamba 2023.