✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta ba ma’aikatu wa’adin mako uku su kare kasafinsu

Hukumomi da ma'aikatun da suka saba wa'adin za su tashi babu ko sisi

Majalisar Dattawa ta ba wa hukumomi da ma’ikatun Gwamnatin Tarayya wa’din mako uku su kare kasafinsu na 2021 daga ranar Juma’a 16 ga Oktoba.

Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan ya ce duk ma’aikata hukumar da ta gaza yin hakan to za ta tashi babu ko sisi a kasafin.

Ahmad Lawan yayin jawabinsa a ranar Alhamis inda Majalisar ta kammala karatu na biyu a kan kasafin ya bukaci hukumomin tare kudaden shiga da su kara azama aikinsu.

Bayan mika kasafin ga kwamitinsa, Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar, Sanata Barau Jibrin yayin jagorantar zaman da ya yi da shugabannin kwamitocin Majalisar ya bukace su da su yi aikin a kan kari domin “akasin haka zai haiwar wa aikin cikas”.

Ya ba da tabbacin kammala aikin kasafin a kan lokaci domin fara aiwatar da shi daga ranar 1 ga watan Janairu, 2021.

Barau Jibrin ya ce Kwamitinsa zai gudanar da zaman sauraron ra’ayoyin jama’a kan kasafin daga ranar 9 zuwa 10 ga watan Nuwamba domin ‘yan Najeriya su tofa albarkacin bakinsu.

Daga ranar 11 zuwa 18 ga watan kuma kananan kwamitoci za su gabatar wa kwamitinsa cikakkun rahotanninsu kan kasafin.

Kwamitin kasafin kuma zai tattara rahotannin a ranar 19 ga Nuwamba sannan ya gabatar wa zauren Majalisar a ranar 20 ga watan.