✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta bukaci CBN ya kara wa’adin daina karbar tsoffin kudi

Majalisa ta ce bai kamata a tilasta wa jama'a karbar dokar cikin takaitaccen lokaci ba.

Majalisar Wakilai ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya sake duba sabbin dokokin hada-hadar kudi da ya fitar da kuma wa’adin 31 ga Janairu da ya bayar na daina amfani da tsoffin kudin da aka sauya.

Bukatar hakan ta biyo bayan kudurin da dan majalisa, Sada Soli Jibia ya gabatar  yayin zamanta na ranar Talata.

Ya ce, “A tsari mafi karbuwa a duniya, shafe kudade akan yi amma ba dakatar da su da karfin tsiya ba.

“Don haka ana bukatar isasshen lokaci don cim ma nasarar  dokar.”

Ya kara da cewa, kamata ya yi CBN ya gabatar da dokokin da za su zama kusa kuma masu yiwuwa da al’umma maimakon hasashe.

A cewarsa, “Duk da dai doka ce mai kyau, amma hakan ba adalci ba ne ga gwamnati mai zuwa wadda ke da bukatar kyakkyawan yanayin da zai taimaka mata wajen bunkasa tsarin hada-hadar kudin kasar.”

“Tilasta wa jama’a kabar dokar ta CBN cikin takaitaccen lokaci ka iya haifar da matsaloli ga tattalin arziki a sassan kasar,” in ji shi.

Daga nan, Majalisar ta bukaci CBN ya samar da wadatattun sabbin takardun Nairar don amfanin ’yan kasa.

Kazalika, ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya sa baki dangane da wa’adian da CBN ya gindaya.