✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa a haramta tallata auren jinsi a Rasha

Dokar dai na bukatar goyon bayan Majalisar Dattijai da kuma sanya hannun shugaba Vladimir Putin.

Majalisar Wakilan Rasha ta amince da sabuwar dokar da ta haramta duk wani yunkurin yada farfagandar da ke goyon bayan auren jinsi a sassan kasar.

Sabuwar dokar wadda a ranar Alhamis aka kada wa kuri’a ba tare da hamayya ba, Mosow ta tsaya kai da fata game matsayarta na haramta duk wata alakar auratayya da ta saba wa yadda dan adam ya gada tsawon shekaru a ban kasa.

Da ya ke jawabi game da sabuwar dokar, Kakakin Majalisar Wakilan ta Rasha Vyacheslav Volodin, ya ce akwai hukunci mai tsauri kan duk wanda aka samu da laifin wanda ya saba da halittar dan adam.

Majalisar ta Rasha cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Telegram, ta ce sabuwar dokar za ta kange al’ummar kasar musamman masu tasowa a nan gaba daga mummunar akidar wadda Amurka da kasashen Turai ke son karfafata a Duniya.

Dokar dai na bukatar goyon bayan Majalisar Dattijai da kuma sanya hannun shugaba Vladimir Putin gabanin fara aiki da ita tare da hukunta wadanda aka samu da wannan dabi’a ko kuma farfagandarta.