✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta kirkiri dokar haramta biyan kudin fansa

Majalisar Dattawa ta zartar da kudirin neman gyaran fuska ga dokar haramta ta’addanci ta 2013, hadi da haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da…

Majalisar Dattawa ta zartar da kudirin neman gyaran fuska ga dokar haramta ta’addanci ta 2013, hadi da haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane a Najeriya.

Wuce karatun da dokar ta 2013 ta yi ya biyo bayan rahoton kwamitin da ke lura da bangaren shari’a da kare hakkin dan Adam.

Rahoton da shugaban kwamitin, Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar ya ce kudirin zai haramta biyan kudin fansa ga masu satar mutane da sauran yan ta’adda domin sakin wani wanda da suka kama ba bisa ka’ida ba.

Haka zalika ya ce an yi hakan ne domin kawo karshen garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da ke sake yaduwa a kasar nan.

Shugaban ya kuma ce an fito da batutuwa daban-daban kan harkar tsaro da suka hada da ta’addanci, yaduwarsa a Najeriya, da masu daukar nauyinsa wadanda suke tafiya da zamani.

Bamidele ya cigaba da cewa: Gyaran dokar zai sanya damba ga hana kungiyoyin yan ta’adda halatta kudin haram ta bankuna, da sauran hanyoyin sarrafa kudi na yanar gizo.”

“Haka kuma samar da dokokin irin wadannan tabbatacciyar hanya ce ta toshe hanyoyin daukar nauyin ta’addanci, da haramtattun hanyoyin sarrafa kudade na yanar gizo,” In ji shi.