✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta nemi a yi wa matasan NYSC karin kudin abinci

Kwamitin Majalisar ya bayyana takaici cewa kudin abincin matasan NYSC bai kai na fursunoni ba

Sanata Smart Adeyemi ya ce ya zama dole Gwamnatin Tarayya ta yi wa matasa masu yi wa kasa hidima karin kudin abinci da kashi 66 cikin 100.

Ya bayyana haka ne a ranar Talata bayan Kwamitin Wasannin da Cigaban Matasa na Majalisar ya bukaci a kara kudin abincin matasan na NYSC daga Naira 600 zuwa Naira 1,000, saboda a halin yanzu kudin abincin fursuna ya kusa ninka nasu.

Shugaban kwamitin, Sanata Obinna Ogba, ya ce, “Abin takaici ne idan har fursunonin da ke tsare a gidan yari saboda sun aikata laifi za su fi matasan NYSC da ke yi wa kasa hidima samun kulawa.

“Bai kamata kulawar da ake ba wa fursuna ta fi wadda ake ba wa mai yi wa kasa hidima ba, amma a halin yanzu kudin abincin matasan NYSC N600 ne a rana, amma na fursuna kuma N1,000.

“Saboda haka nake rokon gwamnati da Majalisa su kara kudin abincin masu yi wa kasa hidima daga N600 zuwa N1,000 sannan su kara ingancin kakin matasan.”

Kalaman na sa na zuwa ne bayan karin da Majalisa ta yi na kudin abincin fursunonin daga N450 zuwa N1,000 a kowace rana.

Da yake mika rahoton kwamitinsa ga Kwamitin Majalisar kan Kasafin 2022, Sanata Ogba ya koka kan abin da ya kira rashin ware wa Ma’aikatar Wasanni da Cigaban Matasa isassun kudade domin gudanar da ayyukanta.

Saboda haka, “Ya kamata a yi abin da ya dace domin babu abin da kasafin zai yi wa ma’aikatar,” inji shi.

Shi ma a nasa tsokacin, Sanata Smart Adeyemi ya ce karin kudin abicin matasan NYSC ya zama dole domin ba su kwarin gwiwar nuna kishin kasa.