✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta nemi Buhari ya ayyana dokar ta-baci a Najeriya

'Yan Najeriya sun shiga cikin halin kakanikayi saboda matsalar tsaro.

Majalisar Wakilai ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana dokar-ta-baci kan harkokin tsaro a fadin tarayya.

Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila, ya bayyana matakin hakan ne yayin zanta wa da manema labarai bayan zaman shugabannin majalisar da ya gudana na tsawon sa’a biyar a ranar Talata.

A cewarsa, majalisar ta yanke shawarar gayyato mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasar, Manjo-Janar Babagana Monguno, Manyan Hafsoshin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a kan kalubalen da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

Mista Gbajabiamila ya kuma ce majalisar ta umarci dukkan muhimman kwamitocinta da su yi bita kan matsalar tsaro da ta addabi kasar domin gano madafar da za a kama wajen samar da zaman lafiya mai dorewa.

Aminiya ta lura cewa majalisar ta yi wannan kira ne da zummar ganin an kawo karshen hare-haren da ke haddasa asarar rayuka da ma dukiyoyi a dukkan sassan kasar.

Ana iya tuna cewa, watanni biyu da suka gabata ne Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaba Buhari ya gaggauta yin shelar kafa dokar ta-baci kan matsalolin tsaron da suka addabi kasar.

Majalisar ta gargadi shugaban ne bayan da ‘yan bindiga suka sace sama da dalibai 200 a wata makarantar Sakandiren Kimiyya ta Kagara da ke Jihar Neja.