✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa Ta Umarci CBN Ya Kara Tsabar Kudin Da Za A Iya Cira

Majalisa ta kuduri aniyar goya wa CBN baya don ci gaba da samar da sauye-sauye

Majalisar Dattawa ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kara yawan tsabar kudin da mutane za su iya cirewa a sabuwar dokarsa ta takaita yawon tsaba a hannun mutane.

A zaman nata ta bukaci Bankin ya kara adadin kudin da za a iya cirewa, saboda koke-koken jama’a da suka biyo bayan ayyana tsarin.

Majalisar ta kuma bai wa kwamitin umarnin sanya ido a kan bankin CBN, don tabbatar da ya daidaita adadin, da kuma mika mata rahoto lokaci zuwa lokaci.

A ranar 9 ga watan Janairu, 2023, CBN zai fara aiwatar da dokar takaita wa mutane cirar tsabar kudi a banki zuwa N500,000 da kuma N100,000 ta cibiyoyin cirar kudi na POS; Kamfanoni kuma za su ciri N500,000 ta POS da kuma N10m ta banki a mako.

Sai dai a muhawarar da majalisar ta yi kan rahoton kwamitinta kan harkokin banki, ta gayyaci Gwamnan Bankin CBN don duba yiwuwar aiwatar da manufar.

Yayin muhawarar dai sanatoci da dama sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan janye dokar CBN din, inda akasarinsu suka amince aiwatar da shi zai shafi tattalin arzikin karkara.

Amma Majalisar ta ce ta kuduri aniyar goya wa CBN baya don ci gaba da samar da sauye-sauyen da za su tallafa wa al’ummar kasar da suka yi daidai da dokokinsa.