✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta yi sammacin Emefiele bayan canjin Dala ya kai N700

Majalisar na bukatar cikakken bayani kan yadda darajar Naira ke ci gaba da faduwa.

Majalisar Dattawa ta gayyaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, don ya yi mata bayani kan faduwar darajar Naira.

Hakan ya biyo bayan kudirin da Sanata Olubunmi Adetunmbi daga (APC, Ekiti ta Arewa) ta gabatar.

A halin yanzu dai canjin Naira na tsakanin N690 zuwa N700 kan kowacce Dalar Amurka daya a kasuwar bayan fage.

Da yake karin haske kan lamarin, Sanata mai wakiltar Neja ta Gabas, Sani Musa, ya ce Naira za ta kara daraja idan ‘yan Najeriya na cin abin da suke nomawa a gida.

A nata bangaren, Sanata mai wakiltar Ekiti ta Kudu, Biodun Olujimi, ta zargi CBN da ba da gudunmawa wajen faduwar darajar Nairar.

Ta ce, “Yawancin abin da ke faruwa shi ne saboda mutane suna fitar da Dala suna sayar da su sannan su dawo da su – ya kamata mu ladabtar da duk wani da muka samu da taimaka wa wajen karyewar darajar Naira.

“Lokaci ya yi da za mu duba abin da ke faruwa. Abin da ke faruwa da Dala, kwatankwacin abin da ke faruwa ne ga Najeriya a yanzu.”

Majalisar ta kuma bukaci babban bankin da ya magance faduwar darajar Nairar a cikin gaggawa.

An amince da kudirin ne bayan Shugaban Majalisar, Sanata Ahmed Lawan ya sa an kada kuri’a.