✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta yi sammacin minista da manyan hafsoshin tsaro kan harin Kankara

Majalisar na bukatar su yi mata bayani kan harin sakandiren Kankara.

Majalisar Dattawa ta gayyaci Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (Mai Ritaya) da Manyan Hafsoshin Tsaro kasa da su bayyana a gabanta don yin cikakken bayani kan yunkurin da suke yi na kubutar da daliban makarantar sakandiren Kankara a jihar Katsina.

Matakin ya biyo bayan kudirin da Sanata mai wakiltar mazabar Katsina ta Kudu a majalisar, Sanata Bello Mandiya ya gabatar a gabanta ranar Talata.

Dan majalisar ya lura cewa harin ya zo ne a lokacin da har yanzu ba a kai ga ceto ’yan mata dalibai 270 na garin Chibok da aka sace tun 2014 ba, da kuma sace wasu sama da 100 a sakandiren Dapchi dake jihar Yobe a 2018.

Ya bayyana damuwar sa cewa muddin ba a dauki matakin da ya kamata wajen ceto yaran ba, za su iya fada wa wani mawuyacin hali a hannun ’yan ta’addan.

’Yan majalisar dai a tsokacin su daban-daban sun nuna takaicin yadda ake ci gaba da samun kashe-kashe da garkuwa da mutane a fadin kasar ba tare da Manyan Hafsoshin Tsaron sun yi wani hobbasa wajen yi wa tufkar hanci ba.

Shugaban Majalisar, Sanata Ahmed Lawan ya yi kira ga takwarorinsa da kada su fusata a kokarinsu na tattauna kalubalen tsaron.

Ya ce, “Babu wani abu mafi muhimmanci ga gwamnati fiye da kare lafiyar al’ummar ta. A zahirin gaskiya ma wannan shine makasudin gwamnati.

“A matsayin mu na masu yin doka, ba za mu taba gajiyawa ko yin kasa a gwiwa wajen tattauna batutuwan da suka shafi mutanen mu ba.

“Mu ma wani bangare ne na gwamnati ko da yake akwai bangaren da aikin mu ya fi mayar da hankali. Dole mu ci gaba da yin magana,” inji shi.

A makon da ya gabata ne dai wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kai hari makarantar sakandiren ta garin Kankara a jihar Katsina tare da yin awon gaba da dama daga cikin daliban ta.

Sai dai a wani sabon sakon murya da Boko Haram ta fitar ta bakin kakakin ta, Abubakar Shekau, kungiyar ta dauki alhakin kai harin tare da sace daliban makarantar.