✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta yi watsi da bukatar karbo bashin $200m don sayen gidajen sauro

Gwamnati na son ciyo bashin $200m don sayen gidajen sauro da magajin maleriya.

Majalisar Dattawa ta yi watsi da bukatar Gwamnatin Tarayya na karbo bashin Dala miliyan 200 domin sayen gidajen sauro da maganin cutar maleriya a kasafin 2022.

Majalisar ta caccaki gwamantin ne a lokacin da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya take kare kasafinta na shekarar 2022 a gaban kwamitin majalisar.

Shugaban kwamitin, Sanata Ibrahim Oloriegbe,  ya ce babu dalilin da za a ciyo bashin Dala miliyan 200 domin yakar cutar maleriya a 2022 alhali an riga an ware Naira miliyan 450 domin hakan.

Sanata Oloriegbe ya kuma caccaki yunkurin sayo gidajen sauron da kamfanoin Najeriya ke iya yi daga kasashen waje, da cewa, “Wannan  ai wata hanya ce kawai ta samar wa ‘yara’ kudade da ayyukan yi. Za a bayar da hannun dama ke nan, a amshe da hannun hagu.”

Tun da fakro da yake gabatar da kasafin, Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Mammam Mahmuda, ya shaida wa kwamitin majalisar cewa karbo rancen yana da muhimmanci, idan aka yi la’akari da yawan rasuwar yara ’yan kasa da shekara biyar, sakamakon kamuwa da cutar maleriya da kuma rashin isasshen maganinta.

A cewarsa, idan aka samu amincewar majalisar, za a yi amfani da Dala miliyan 200 din ne wajen saye da kuma raba gidajen sauro da maganin cutar maleriya a jihohi 13 da ke fama da karancinsu.

Sai dai kwamitin majalisar ya caccaki Babban Sakataren ma’aikatar da Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA), a kan hakan.

Shugaban kwamitin, Sanata Ibahim Oloriegbe, ya ce, “Ya kamata a matsayinmu na kasa, mu rika kera abin da mutanenmu za su yi amfani da shi.

“Idan ma mutum zai ba mu bashi, idan ya gindaya mana sharadi cewa dole sai mun sayi kayan daga kamfanonin kasarsa, mu ce masa a’a domin tsare ’yancin kasarmu.”

Don kwamitin ya bukaci karin bayani game da batun karbo bashin, ya kuma ce jami’an ma’aikatar lafiya su tafi, sai sun sake nemansu wani lokaci.