✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta yi watsi da dokar hana ’ya’yan masu mukaman siyasa karatu a kasar waje

’Yan majalisa sun ce tun kafin su samu mukaman siyasa ’ya’yansu ke karatu a kasashen waje

Majalisar Wakilai ta watsi da kudirin dokar takaita kai ’ya’yan masu rike da mukaman siyasa da jami’an gwamnati karatu a kasashen waje.

’Yan majalisar sun yi ca a kan kudurin dokar wadda ta bukaci a karfafi cibiyoyin ilimi mallakar gwamnati a Najeriya, daga barazanar da suke fuskanta daga na kasashen waje da suke ta yawaita a kasar.

A martaninsa ga kudurin dokar, Honorabul Leke Abejide, ya ce: “Shin ana nufin sai in cire ’ya’yana daga makarantun da suke a kasar waje ke nan, duk da cewa tun kafin in zama dan Majalsiar Wakilai suke karatu a can?”

Ya bayyana cewa daga cikinsu akwai wadanda tun kafin su zama masu rike da mukaman siyasa ’ya’yansu ke karatu a kasashen waje don haka babu dalilin yin dokar.

Amma mai gabatar da kudirin, Honorabul Sergious Ogun, ya bukaci ’yan Majalisar su karanta kudurin dokar a natse su fahimci duk da ta kunsa, ba wai su tsaya a kan abu daya ba.

Honorabul Ogun ya bayyana cewa manufar dokar ita ce taka burki ga yadda jami’an gwamnati da masu rike da mukaman siyasa suke tura ’ya’yansu karatu a kasashen waje ba tare da sun yi abin da ya kamata ba wajen inganta makarantun gamnati ba na cikin gida

Daga karshe dai Majalisar ta yi watsi da kudurin a lokacin karatu na biyu a kansa da suka yi a zaman da Mataimakin Shugaban Malisar, Honorabul Ahmed Idris, ya jagoranta a ranar Alhamis.