✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa za ta binciki dan sandan da ya kashe lauya a Legas

Dan sandan ya harbe lauyar har lahira a ranar Kirsimeti.

Majalisar Wakilai ta yanke hukuncin gudanar da bincike kan kisan da wani dan sanda ya yi wa wata lauya, Misis Bolanle Raheem a Jihar Legas.

Majalisar ta ba da umarnin gurfanar da jami’in cikin gaggawa don yi wa wadda ya kashe adalci.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa da dan Honorabul Ibrahim Obanikoro ya gabatar.

Dan majalisar ya gabatar da kudurin, inda bukaci a haramta wa ’yan sanda shan giya da aikata dabi’u marasa kyau a yayin da suke bakin aiki.

Yayin da yake yanke hukunci kan kudirin, Shugaban Majalisar Femi Gbajabiamila, ya bayyana kisan a matsayin abun takaici.

Tuni aka kama dan sandan mai mukamin ASP bisa zargin sa da kisan lauyar kuma mai harkar gidaje, Bolanle Raheem, a ranar Kirsimeti.

A yayin da lamarin ya faru dai, dan sandan na tare da wasu abokan aikinsa su biyu a unguwar Ajah da ke Jihar Legas.

Aminiya ta ruwaito cewa Bolanle na tare da ’yar uwarta da ’ya’yanta su hudu, lokacin da suke kokarin ficewa daga wani wajen cin abinci, a lokacin da dan sandan ya bindige ta a karkashin gadar Ajah.

Rahotanni sun ce dan sandan ya harbi wata mota ce da ke tafiya, inda harsashin ya same ta.

An ce ta rasu a asibiti ne bayan an garzaya da ita.