✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa za ta kara harajin makarantun gaba da sakandare

Kwamitin Ilimi na Majalisar Dattijai ya ce akwai bukatar karin harajin makarantun gaba da sakandare  daga kashi 2.5  zuwa uku, domin inganta ayyukan gwaje-gwaje da…

Kwamitin Ilimi na Majalisar Dattijai ya ce akwai bukatar karin harajin makarantun gaba da sakandare  daga kashi 2.5  zuwa uku, domin inganta ayyukan gwaje-gwaje da bincike a Najeriya.

Kwamitin ya bayyana hakan ne yayin ziyararsa ga Shugabannin Asusun Tallafa wa Makarantun Gaba da Sakandare (TETFUND), domin duba ayyukan kasafin hukumar na 2021/2022.

Kwamitin, karkashin jagorancin Sanata Ahmad Babba Kaita, ya bukaci TETFUND ya sanya Cibiyar Lissafi ta Kasa (NMC) a jerin wadanda za su dinga bai wa tallafin, domin babu wata kasa da za ta ci gaba a fannin bincike da kimiyya da fasaha da kuma kirkire-kirkire, ba tare da ta rungumi ilmin lissafi ba.

Ya kuma ce akwai bukatar Hukumar ta kara dagewa wajen samar da na’urar bada iskar Oxygen da a baya Kwalejin Fasaha ta Kaduna ta bukata, lokacin da duniya ta yi fama da cutar COVID-19.

A nasa Bangaren Babbabn Sakataren TETFUND Sonny Echono, ya ce, tuni hukumar ta amince da fitar da N50m domin fara samar da iskar, har ma ta biya rabin kudin.

Haka kuma ya ce a 2021 kadai, hukumar ta raba wa makarnatun gaba da sakandare tallafin Naira biliyan 213, ciki har da sabbi da suka fara aiki a shekarar.