✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dattajai ta yi barazanar zaftare kasafin kudin ma’aikatu 100

Majalisar ta ba su mako daya su bayyana, ko su hana su ko sisi a 2023

Majalisar Dattijai a ranar Laraba ta yi barazanar zaftare kudaden da ake ba wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati saboda gaza amsa wasu tambayoyin da Ofishin Babban Mai Bincike na Tarayya ya yi musu.

Shugaban majalisar, Sanata Ahmed Lawan ne ya bayyana hakan, bayan Shugaban Kwamitin Bincike na Ayyukan Gwamnati, Matthew Urhoghide (PDP, Edo) ya gabatar da korafi yayin zaman majalisar cewa hukumomin da aka nuna wa yatsa a cikin binciken sun ki su bayyana a gaban kwamitinsa.

Sanata Matthew ya ce a lokuta daban-daban, kwamitin nasa ya sha gayyatar shugabannin ma’aikatu da hukumomin, amma sun yi kunne uwar shegu.

Ya ce sassa na 88 da na 89 na Kundin Tsarin Mulki ya ba majalisar damar aike wa hukumomin sammaci don su ba da ba’asi kan kudaden da suke kashewa.

Da yake mayar da jawabi, Sanata Ahmed Lawan, ya ba ma’aikatun da lamarin ya shafa mako daya su bayyana a gaban kwamitin ko a hana su ko sisi a kasafin kudin 2023.

“Ina amfani da wannan damar in ba da shawara cewa nan da mako daya mai zuwa, hukumomin da lamarin ya shafa su bayyana a gaban kwamitin. Idan ba su yi cikakken bayani ba sannan ba su bayar da kwakkwaran dalili ba, za mu zaftare kasafinsu,” inji Shugaban Majalisar ta Dattawa.

Wasu daga cikin hukumomi da ma’aikatun da lamarin ya shafa sun hada da Ofishin Babban Lauyan Gwamnati da Ma’aikatar Cikin Gida da ta Harkokin Waje da ta Kudi da ta Sufuri da ta Lafiya da ta Ayyuka da Gidaje da ta Yada Labarai da Al’adu da ta Tama da Karafa da ta Harkokin ’Yan Sanda da ta Tsaro da ta Matasa da Wasanni da ta Man Fetur da kuma ta Sufurin Jiragen Sama.

Sauran sun hada da Fadar Shugaban Kasa da Ofishin Kasafin Kudi da Rundunonin tsaro na sojojin sama da ta ruwa da ta kasa da hukuma NAFDAC da NSCDC da FERMA da NEMA da NAHCON da NHIS da NECO da NACA da NIA da dai sauransu.